Gwamnatin Borno zata yi bincike akan ambaliyar Maiduguri

0
32

Gwamnatin jihar Borno ta ce zata yi bincike akan musabbabin faruwar ambaliyar ruwan Maiduguri.

Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, shine ya kafa kwamitin mutanen da za su yi binciken sanadin faruwar ambaliyar da tafkin Alau yayi kwanaki, don hana faruwar hakan a nan gaba.

Karanta karin wasu labaran:Yan Boko Haram sun yanka manoma a jihar Borno

Ballewar da tafkin Alau yayi a watan daya wuce tayi sanadiyyar samun ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri da kananun hukumomin dake kusa da birnin.

Akalla mutane miliyan 2 ne suka rasa muhallin su saboda faruwar lamarin, sannan wasu da dama suka rasu, tare da yin asarar duniya mai yawan gaske.

An gina tafkin Alou, a tsakanin shekarun 1984 zuwa 1986, da manufar samar da ruwan da za’a rika amfani da shi wajen noman rani da amfanin yau da kullum ga al’ummar dake kusa da tafkin.

Sakataren gwamnatin jihar Alhahji Bukar Tijani, a daren jiya ya sanar da cewa mutanen da zasu shugabanci kwamitin sun kunshi masana harkokin kimiyya da injiniyoyi.

Za’a kaddamar da kwamitin da misalin karfe 2 na ranar yau asabar a gidan gwamnatin jihar Borno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here