Mahaifin Wizkid yayi magana akan rikicin dan sa da Davido

0
79

Munir Balogun, mahaifin fitaccen mawakin nan dan Nigeria Wizkid ya yi magana akan rikicin dake faruwa tsakanin dan sa Wizkid da abokin Sana’ar sa David Adeleke wanda akafi sani da Davido.

 A yan kwanakin nan masu amfani da shafukan sada zumunta sun gano yadda mawakan biyu ke samun sabani da juna.

Karanta karin wasu labaran:Farashin Dala a yau

Daukacin mawakan da magoya bayan su sun afka cikin rikicin a shafin sada zumunta dangane da batun wanda yafi wani shahara da magoya baya a tsakanin su.

Mahaifin Wizkid, yace ya ziyarci shafukan sada zumunta sannan ya ganewa idon sa duk abubuwan dake faruwa, sannan ya bawa Wizkid shawarar yanda zai yi akan rikicin nasu.

Yace daga cikin shafukan sada zumuntar daya shiga akwai Facebook da Instagram, kuma ya fahimci abinda kowa yake cewa.

Daga cikin shawarar da mahaifin Wizkid ya bashi, yace kar dan nasa ya saurari duk maganganun da magoya bayan Davido, zasu yi akan sa.

DAVIDO WIZKID

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here