Murtala Sule Garo, tsohon kwamishinan kananun hukumomin jihar Kano, kuma dan takarar mataimakin gwamnan jihar na jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023, yayi fice tare da yin suna wajen yin aikin kirki da taimakon mutane.
Bayan kwarewar da yake da ita a siyasan ce ya kuma taka rawar gani a fannin cigaban al’ummar kauyuka, sannan ya kasance mai tasiri a kowanne bangare.
A lokacin da Garo, ya rike mukamin kwamishinan kananun hukumomi ya taka rawar gani tare da inganta rayuwar mutanen Kano.
Ya kuma mayar da hankali a fannin cigaban ilimi da kuma yiwa bangaren Ilimin garambawul, wanda hakan yayi matukar tasiri musamman a yankunan karkara.
Karanta karin wasu labaran:Kotu zata yanke hukuncin hana Sarkin Kano na 15 gyara gidan Nassarawa
Daya daga cikin muhimmiyar gudummawar da Garo ya bayar ita ce rawar da ya taka wajen gyarawa da gina wuraren bayar da ilimi a Kano.
Ya samu sahalewa daga tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda a wancan lokaci ya amince aka samar da kudaden da aka yi gyare-gyare a makarantun dake fadin kananun hukumomin jihar Kano 44.
Wannan aiki da Garo, ya kirkiro shine ya tabbatar da samun nasarar bawa kananun yaran dake kananun hukumomin Kano ilimi mai inganci a wancan lokaci.
Garo ya ce Ilimi shine ginshikin kowace al’umma mai son cigaba, kuma mun ba shi fifiko wajen tsara manufofinmu.
A yunkurin nasa, tare da karin ayyukan samar da ababen more rayuwa, ya ba da gudummawa wajen habbaka ilimi mai nagarta a fadin Kano.
Bayan samun nasara a fannin ilimi, Murtala Sule Garo ya kuma taka rawa sosai wajen samar da ababen more rayuwa a jihar Kano, musamman wajen inganta hanyoyin sifuri.
A karkashin jagorancinsa, masu rayuwa a kauyuka sun amfana da gina tituna da manyan gadoji wanda aka yi hakan don saukaka zirga-zirgar mutane da bunkasa tattalin arziki yankin karkara.
Ayyukan da yayi sun hadar da gina hanyar Garo zuwa Gadinya a karamar hukumar Kabo, wadda ta zama mai muhimmanci a tsakanin al’ummar dake rayuwa a yankin.
Wadannan ayyukan ababen more rayuwa sun inganta sufurin kayayyaki sosai, wanda hakan ya kawo sauki ga manoma da ‘yan kasuwa wajen samun bunkasar tattalin arzikin yankin.
Gudummawar Murtala Sule Garo, ba ta tsaya akan abubuwan more rayuwa kadai ba, Sakamakon cewa an san shi da dimbin shirye-shirye na karfafa gwiwa da nufin kawar da talauci, musamman a tsakanin matasa da matan Kano.
Ta sanadiyyar shirye-shiryen, sa sama da mutane 1,200 a karamar hukumar Kabo sun samu jarin fara sana’o’i, da motoci, don taimaka musu wajen fara yin kasuwancin da zasu dogara da kan su.
Garo, yace a matsayin sa na wanda ya San irin halin da matasa ke ciki ya bayar da muhimmanci wajen samar da abubuwan da suke bukata musamman na Sana’ar da zasu samu cigaba da daukaka.
Yace wadannan tsare-tsare ba su tsaya akan inganta rayuwar jama’a kadai ba, sai dai sun kunshi samar da kasuwanci a yankunan karkara da Kuma koyon sana’o’in dogaro da kai.
A matsayinsa na dan takarar mataimakin gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023, Garo yana da kwarewa da cancantar samun takarar.
Sakamakon cewa ya jima a cikin siyasa Kuma ya fara yin siyasar tun daga tushe Garo, ya zama mai son cigaban al’umma hakan tasa ya zama fahimtar bukatun al’umma.
Magoya bayan sa sun bayyana shi a matsayin jarumi wanda ba ya tsoron yin tsayin daka don kare rayuwar al’umma, da Kuma fuskantar kowanne irin kalubalen yanayin siyasa.
A taÆ™aice dai, gudunmawar da Murtala Sule Garo ya bayar wajen ci gaban Kano, musamman a fannin ilimi, da samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar matasa, sun bar tarihin da ba za’a iya mantawa dashi ba.
Yayin da a yanzu ya ci gaba da fafutukar tafiyar siyasa, ko shakka babu mayar da hankalin sa da jajircewar sa zai samarwa jihar Kano gobe mai kyau.
ReplyForwardAdd reaction |