Gwamnan Kano ya samu lambar yabo akan cigaban ilimi

0
44

Ƙungiyar Malamai ta kasa (NUT), ta bawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf lambar yabo saboda  gudunmawar da ya bayar wajen gyaran harkar ilimi a jihar.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar ta bayyana cewa an ba da lambar yabon ne a bikin ranar Malamai ta Duniya ta 2024 da aka yi a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Kranta karin wasu labaran:APC ta sake shigar da kara kan zaben kananun hukumomin Kano

Dawakin-Tofa, ya bayyana cewa an shirya bikin ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta gwamnatiin tarayya, inda aka tara malamai daga jihohi 36 na Kasar nan don karrama wadanda suka bayar da muhimmiyar gudunmawa a fannin inganta ilimi.

An karrama Abba Yusuf saboda kokarin da ya yi na gyara tsarin ilimi a Jihar Kano daga durƙushewa.

Shugaban kungiyar NUT na ƙasa, Kwamared Titus Ambe, ya bayyana cewa gwamnoni guda shida aka karrama bisa jajircewarsu wajen inganta harkar ilimi, musamman ta hanyar tallafawa walwalar malamai.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, daga cikin nasarorin da Gwamna Yusuf ya cimma sun kunshi ware kaso 29.9 na kasafin kuÉ—in Kano na shekarar 2024 ga ilimi.

Da yake magana a madadin gwamnoni shida da aka karrama daga jihohin Borno, Oyo, Benuwe, Enugu, da Kebbi, Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa zai ci gaba da inganta harkar ilimi har karshen mulkin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here