Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA sun kama wata yar kasar Canada, mai suna Adrienne Munju, yar shekara 41, ta shigo da muggan kwayoyi cikin kasar nan.
Munju, ta shiga hannun jami’an ne a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Murtala Muhammad, dake jihar Legas.
Karanta karin wasu labaran:NDLEA ta cafke mai safarar hodar iblis a Legas
An kama wadda ake zargin lokacin da ake yi mata binciken kayan data shigo da su a cikin filin jirgin bayan isowar ta Nigeria a ranar 3 ga watan da muke ciki.
Cikin wata sanarwar da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta fitar a yau ta hannun Kakakin ta Femi Babafemi, yace an kama matar da kunshi 74 na kayan maye da nauyin su yakai kilogram 35.20, a cikin jakunkuna 2.
Da take jawabi tace sun yi ciniki da wani ta kafar internet cewa in ta kawo kayan kasar nan lafiya za’a biya ta dala dubu 10.
Tace tana son biyan kudin rijistar digirin ta na biyu a Canada kuma bata da kudi shi yasa ta dauki wannan kasada.