NYSC ta bayyana dalilin rashin biyan yan bautar kasa sabon alawus

0
32

Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima NYSC ta ce samun jinkirin fara biyan sabon alawus din masu yi wa kasa hidima, da aka gani ya samo asali sakamakon yadda gwamnati ba ta turawa wa hukumar kudin da za’a biya sabon karin ba.

Shugaban hukumar Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed, ya ce a hukumance sun samu takardar amincewa da karin, amma har yanzu ba’a tura kudin fara biyan sabon alawus din ba, daga gwamnatin tarayya.

Karanta karin wasu labaran:‘Labarin tura ‘yan NYSC zuwa Nijar ba gaskiya ba ne’

Dogara yace ko ma’aikatan hukumar NYSC suma an yi musu karin, kusan watanni 5 da suka wuce amma har yau ba a fara biyan su ba.

Sai dai yace suna saka rai nan ba da jimawa ba, za a fara biyan sabon alawus din.

A cikin watan da ya gabata ne hukumar NYSC ta fitar da sanarwar yin kari a alawus ga masu yi wa kasa hidima daga naira 33,000 zuwa 77,000.

Sanarwar ta ce karin sabon alawus din zai fara aiki daga watan Yulin wannan shekarar, abin da ke nuna cewa masu yi wa kasa hidimar za su samu a biya su karin kudin na watanni akalla wata uku da ya wuce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here