Sheikh Gumi yace jami’an gwamnati ne suke raka shi wajen yan ta’adda

0
95

Fitaccen malamin addinin Islamar nan Sheikh Ahmad Gumi, yace jami’an gwamnatin tarayya ne suke yi masa rakiya zuwa wajen yan ta’adda a duk lokacin da zai je wajen su yin tattaunawar samar da yin sulhu.

Gumi, ya kasance mai son a yiwa yan ta’addan da suka addabi al’umma afuwa, da tattaunawa dasu don samun zaman lafiya.

A tattaunawar sa da jaridar Punch, Malamin ya kuma ce wasu daga cikin masu rike da sarautar gargajiya suna raka shi wajen yan ta’addan a wasu lokutan har da jami’an gwamnatin jihohi.

Karanta karin wasu labaran:Yan ta’adda sun kaiwa masu Sallar juma’a hari a Katsina

Yace abin da yake so yan Nigeria su sani shine bai taba zuwa wajen yan fashin daji shi kadai ba, sai dai yana zuwa tare da jami’an gwamnati, da jami’an tsaro saboda ba zai taba yiwuwa mutum daya ya tunkari yan fashin dajin kai tsaye ba.

Buri na shine samar da sasanci da zaman lafiya, saboda masu aikata laifin sun bamu damar tattaunawa da su, inji Gumi.

Da aka tambaye shi akan zargin yan siyasa da daukar nauyin masu tayar da hankalin al’umma, cewa yayi zancen ba haka bane, sannan yace Wannan abu ne da yazo sakamakon kin kulawa da rayuwar masu aikata laifin da aka yi tsawon lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here