An gurfanar da wanda zai kashe kansa saboda yan uwansa sun ki taimaka masa

0
90

An gurfanar da wani matashi mai suna Adamu Mainasara, a kotun Majistri mai lamba 4. dake unguwar Gyadi-Gyadi, a birnin Kano, inda ake tuhumar sa da zargin yunkurin kashe kansa da fetur.

Mainasara, yayi kokarin kashe kansa lokacin daya je garin Dangwauro, sannan ya zuba fetur a jikin, amma yan sanda sun kama shi kafin ya kunnawa kansa wuta.

Karanta karin wasu labaran:Cutuka masu yaduwa sun mamaye Kano Jigawa, Lagos da Oyo.

Lokacin da ake zantawa dashi a harabar kotun yace, dalilin sa na aikata haka shine ya aikawa wani dan uwansa mai wadata sakon irin halin da yake ciki na kunci, sannan dan uwan nasa baya taimaka masa, duk da cewa yana da damar tallafa masa.

Lauyar gwamnati Wahida Ismail, ta zayyano masa abin da ake zargin sa da aikatawa sai dai ya musanta zargin, inda ya jaddada cewa ba kashe kansa yayi niyya ba, sako kawai ya aikewa yan uwan sa akan kuncin da yake ciki.

Mai shari’a Rakiya Lami Sani, ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga Nuwamba, tare da umarnin a cigaba da tsare Mainasara a gidan gyaran hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here