Gwamnan Kano ya gana da Kawu Sumaila da Rurum

0
82
Abba Gida Gida
Abba Gida Gida

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya gana da wasu daga cikin fusatattun yan majalisar dokokin kasa na jam’iyyar NNPP masu kalubalantar wasu kudurorin gwamnatin Kano.

Kamar yadda aka hango wallafa batun ganawar a shafin Facebook na gwamna Abba, ya ce zasu tattauna wasu batutuwa masu muhimmanci da yan majalisar akan abubuwan da suka shafi jihar Kano, da Jam’iyyar NNPP.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnan Kano ya samu lambar yabo akan cigaban ilimi

Majiyar jaridar Daily Post, ta tabbatar da cewa yan majalisar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya gana dasu sun hadar Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar kudancin Kano, sai wakilin Rano Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, da aka tabbatar wa da jaridar cewa suna kan hanyar ficewa daga jam’iyyar NNPP.

Daga cikin dalilan su na son fita daga NNPP akwai zargin karfin ikon da aka ce Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, yana nunawa a harkokin tafiyar da gwamnatin Kano, da kuma rage darajar masarautun da tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya samar zuwa masu daraja ta biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here