Gwamnatin tarayya ta cire baki dayan tallafin man fetur

0
82

Daga ranar Alhamis mai zuwa yan kasuwa masu dillancin man fetur zasu fara siyan man daga Matatar Dangote kai tsaye ba tare da kamfanin NNPCL ya shiga tsakanin su ba.

A ranar talata ne aka samu tabbacin hakan daga majiyoyi da dama na kamfanin NNPCL da Kuma bangaren dillalan man, na cewa za’a kyale yan kasuwar da Dangote suyi ciniki babu saka takunkumi.

Karanta karin wasu labaran:NNPCL ya bawa Matatar Dangote gangar mai miliyan 48

Wannan bayani yazo a daidai lokacin da ake yada jita jitar cewa hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa NMDPRA, ta fitar da sanarwar sabon farashin litar man, wanda ya zarce farashin da ake siya a yanzu.

Amma mai magana da yawun hukumar NMDPRA, George Ene-Ita, bai tabbatar da labarin ba lokacin da aka tuntube shi.

 Yan kasuwar sun ce Wannan janye hannu da kamfanin NNPCL yayi daga harkokin siyar da fetur tsakanin yan kasuwa da Dangote ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta dena biyan tallafin man fetur kwata kwata.

A watan Satumba wani rahoton ya nuna cewa a kowanne wata gwamnatin tarayya tana kashe naira biliyan 236, a matsayin kudin tallafin fetur.

Sannan a cikin Wannan kudi ana biyan matatar man Dangote tallafin naira biliyan 99 a kowanne wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here