Hisbah ta kama masu bude shagunan yin caca a cikin unguwanni

0
93
Hisbah
Hisbah

A ranar talata, ne hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi nasarar kama wasu mutane da ake zargi da bude shagunan yin caca a unguwar Dakata dake karamar hukumar Nassarawa.

 An kama masu shagunan cacar guda biyu tare da kayan aikinsu, da kuma mutane goma sha biyu suna tsaka da yin cacar.

An samu nasarar kama su lokacin da jami’an Hisbah suka isa wajen bayan samun labarin irin abubuwan da ake aikatawa a Wannan waje.

Karanta karin wasu labaran:Hisbah ta kama kayan mayen da ake yin safarar su Zuwa Adamawa

 Wannan kamen ya biyo bayan wani cikakken bayanin sirri da hukumar ta samu game da yadda ake gudanar da haramtacciyar Sana’ar caca a unguwar ta Dakata.

Hukumar Hisbah ta mika wadanda aka kama zuwa ga kotu, inda ake sa ran za su fuskanci hukunci bisa dokokin shari’ar Muslinci.

Wannan na daga cikin kokarin hukumar na dakile ayyukan da suka saba wa koyarwar Musulunci da kuma al’adun mutanen Kano.

Mukaddashin Babban Kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya yi jan hankali kan illar caca ga addini da al’umma baki daya. 

Ya bayyana cewa caca haramun ce a addinin Musulunci, kuma gwamnatin Kano ta dauki tsauraran matakan tabbatar da cewa irin wadannan ayyuka ba za su ci gaba da tafiya a jihar Kano ba.

Dr. Mujahiddin Aminudden, ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta tare da hadin gwiwar jama’a domin kawar da duk wasu ayyukan da za su iya jefa al’umma cikin fitina ko barazana ga zaman lafiya da ci gaban jihar.

Ya kuma yi kira ga iyaye da malamai da su rika sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu, domin gujewa fadawa cikin irin wadannan mummunan dabi’u, wanda ke kara haifar da tabarbarewar al’umma.

Bude wuraren caca da shaye shaye cikin unguwanni na taka rawa wajen lalata tarbiyyar al’umma musamman yara da matasa masu tasowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here