Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta kalubalanci sabon karin farashin man fetur da gwamnati tayi a yau laraba.
Ƙungiyar tace akwai rashin nuna kwarewa idan aka bari kamfanin da yake zaman kansa ya rika kayyade farashin man.
Karanta karin wasu labaran:An kama shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC
A tsakar ranar yau laraba ne aka gano kamfanin NNPCL ya canja farashin litar man daga naira 898 zuwa naira 1030.
Da yake martani akan sabon farashin shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero, ya nuna mamakin sa akan wane dalili ne yasa a kowanne wata sai an kara farashin man, sannan har yanzu an kasa biyan mafi karanci albashi da aka amince da shi.
Ajaero, yace gwamnatin tana kara farashin ba bare da kawo wa yan kasa hanyoyin magance matsin rayuwar da hakan yake haifar wa ba.