Gwamnatin Kano ta tallafawa yan kasuwar kantin kwari

0
66
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da tallafin naira miliyan 100, don taimakawa yan wadanda da suka yi asara a gobarar kasuwar kantin kwari a makon daya gabata.

Gwamnatin ta bayar da tallafin ne lokacin da gwamna Abba ya kai ziyarar jajantawa yan kasuwar.

Yace manufar samar da tallafin shine a ragewa mutanen da abun ya shafa radadin asarar da suka yi, saboda kudin ba zai biya asarar da aka yi ba

Sannan gwamnatin tayi alkawarin daukar matakan kiyaye afkuwar tashin gobarar a nan gaba.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnan Kano ya gana da Kawu Sumaila da Rurum

Gwamna Abba yace za’a samar wa kasuwar wutar kan hanya mai amfani da hasken rana, da gyara hanyoyin kasuwar, sai hanyoyin ruwa, da kuma samar da rijiyoyin burtsatse.

Shugaban kasuwar Alhaji Hamisu Sa’ad Dogon nama, yace Shaguna 29, wutar ta shafa, amma an samu nasarar shawo kan wutar akan lokaci saboda daukin gaggawa da jami’an hukumar kashe gobara suka kawo.

Shugaban kwamitin iyayen kasuwar Alhaji Sabi’u Bako, ya yabawa gwamnan akan tallafin daya bayar, tare da neman gwamnatin Kano ta magance wa kasuwar sauran matsalolin da ke damun ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here