Kotu ta hana cire shugaban PDP daga mukamin sa

0
66

Babbar kotun tarayya dake birnin Abuja, ta dakatar da jam’iyyar PDP daga cirewa ko dakatar da shugaban jam’iyyar Umar Damagum, daga mukamin shugaban PDP na riko.

Mai shari’a Peter Lifu, ne ya bayar da umarnin dakatarwar, ga kwamitin zartarwa na PDP a matakin kasa daga cire Damagum.

Wasu fusatattun magoya bayan PDP Umar Maina, da Zanna Gaddama, ne suka shigar da karar neman dakatarwar a yau juma’a.

Karanta karin wasu labaran:Jam’iyyar PDP ta dakatar da shugaban ta na kasa

A safiyar yau be Jam’iyyar adawa ta PDP mai fama da rikicin cikin gida ta dakatar da shugaban rikon ta na kasa Umar Damagum, da sakataren ta Samuel Anyanwu, akan zargin su da bijirewa umarnin jam’iyyar.

 Tun da farko shugabancin Damagum, ne ya fitar da sanarwar dakatar da sakataren yada labarai na PDP Debo Olagunagba, da mai bawa jam’iyyar shawara akan harkokin shari’a Kamaldeen Ajibade, inda suka ce sun bijirewa umarnin PDP.

Haka ne yasa suma wadanda aka dakatar din fitar da wata sanarwar da sanyin safiyar yau juma’a cewa sun dakatar da Damagum da Anyanwu.

Daraktan yada labaran PDP na kasa shine ya sanar da batun dakatar da su Olagunagba Chinwe Nnorom.

Rikicin cikin gida dai ya mamaye jam’iyyar PDP, inda ake zargin hannun wasu yayan jam’iyyar da cin amanar ta, ta hanyar hada kai da jam’iyyar APC mai mulkin kasa, sakamakon cewa har mukami APC ta bawa wasu daga cikin yayan PDP.

Batun shirya babban taron jam’iyyar na kasa na daga cikin manyan abubuwan da suka kawo rashin jituwa tsakanin mambobin PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here