Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya tafi birnin Paris na kasar Faransa daga birnin Landan na Birtaniya a ranar Juma’a.
Mai bawa shugaban kasar shawara akan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari ne ya bayyana hakan bayan ya ziyarci Tinubu a Landan.
Ya bayyana a shafin sa na X cewa sun tattauna da shugaban a gidan sa dake birnin Landan.
Daga nan kuma sun wuce birnin Paris na Faransa domin yin wasu ayyuka.
Karanta karin wasu labaran:Shugaban Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 6.45
A ranar 2 ga watan Oktoba ne Tinubu ya tafi Birtaniya domin yin hutun mako biyu, kamar yadda fadarsa ta bayyana a lokacin, amma ba ta ce zai je Faransa ba a tafiya hutun.
Sanarwar ta ce, zai komo gida Nigeria da zarar hutun ya kare.
Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Tinubu ya É—auki hutu tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, duk da cewa ya yi tafiye-tafiyen kasashen waje da dama daga lokacin zuwa yanzu.
Kafin yanzu wasu daga cikin yan Nigeria sun rika yada jita jitar cewa shugaban kasar bashi da lafiya.