Za’a shafe kwanaki uku ana yin mamakon ruwa sama—NIMET

0
49

Hukumar kula da hasashen yanayin ta kasa tayi hasashen samun ruwan sama da tsawa a jihohin kasar nan daga ranar lahadi zuwa Talata 

Hasashen hukumar NIMET, da ta fitar ranar asabar yace a ranar lahadi wasu bangarorin jihohin Gombe, Bauchi, Adamawa, da Taraba, zasu fuskanci matsakaicin ruwan sama da tsawa.

Haka zalika a mafi yawancin yankunan Adamawa, Kaduna, Sokoto, Bauchi, Gombe, Taraba, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara, Borno da Yobe suma za’a samu saukar ruwan.

Karanta karin wasu labaran:Ba’a san Fulani da tashin hankali ba—-Sarkin Zazzau

Sannan suma jihohin dake kusa da birnin tarayya Abuja da birnin na Abuja zasu samu saukar ruwan da sanyin safiya.

Yayin da a jihohin kudu da suka hadar da Oyo, Imo, Enugu, Ogun, Osun, Ondo, Edo, Delta, Rivers, Akwa Ibom, Cross River da Lagos, za’a samu yayyafi da tsawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here