Ba’a san Fulani da tashin hankali ba—-Sarkin Zazzau

0
120

Mai martaba sarkin Zazzau Nuhu Bamalli, yace da zaman lafiya aka san Fulani a Nigeria ba da tashin hankali ba.

Sarkin ya bayyana hakan a ranar asabar lokacin da yake jawabi a wajen taron al’adar fulani wanda kungiyar cigaban al’adun fulani FUDECO, ta shirya, inda sarkin yace fulanin asali ba zasu yi amfani da bindiga wajen aikata ta’addanci ba.

Karanta karin wasu labaran:Sabbin nade-nade a Jama’atu Nasril Islam daga masarautar Zazzau

A cewar sa fulani sun fi kwarewa wajen daukar sanda da wuka domin yin kiwon dabbobi.

Sarkin, ya nemi Fulani su cigaba da yin riko da al’adun su.

Ina yin alfahari da kasancewa ta bafulatani, sakamakon iyaye na fulani ne kuma sun yi rayuwa mai inganci dan haka babu abinda zai hana ni yin alfahari da fulani, inji Sarkin na Zazzau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here