Daya daga cikin bangarorin jam’iyyar PDP ya amince da Ahmad Yayari Muhammad, a matsayin sabon shugaban rikon jam’iyyar PDP a matakin kasa.
Yayari, shine ya sanar da karbar ragamar jam’iyyar a yau lahadi.
Bangaren dake kalubalantar shugabancin Illiya Damagum, ne suka nada Yayari.
Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana cire shugaban PDP daga mukamin sa
A cikin wata sanarwa da Yayari, ya fitar a yau yace PDP ta gaza yin abun da ya dace na taka rawa a matsayin babbar jam’iyyar adawa, yana mai cewa a karkashin jagorancin sa kwamitin ayyukan PDP na kasa zai tabbatar da bin dokokin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Ahmad Yayari, yace shugabancin sa zai yiwa kowa adalci ba tare da duba mataki ko matsayin mutum ba.
Zan yi kokarin samar da kwarin gwiwa a tsakanin magoya bayan PDP, da kuma shirin gudanar da babban taron kwamitin zartarwa na PDP a matakin kasa ranar 24 ga watan Oktoba, inji Yayari.
Sannan yace in aka yi duba akan kundin tsarin mulkin PDP yankin arewa ta tsakiya ne zai samar da sabon shugaban jam’iyyar.