Nigeria zata shiga matsanancin rashin fetur—–IPMAN

0
82
Man fetur a Najeriya

Ƙungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta nesanta kanta da cewa ita ce musabbabin ci gaba da ganin dogwayen layukan motoci a gidajen mai, sakamakon karancin man da ake fama da shi duk da matakin gwamnatin tarayya na sake kara farashin man, har yanzu tsadar bata hana man yin karanci ba.

A cewar IPMAN, an samu sabanin fahimta tsakaninta da kamfanin mai na NNPCL, duba da yadda kamfanin a yanzu ya ke sayar da mai a farashi mai tsada ga yan kasuwa ko kuma mambobin kungiyar akasin farashin da ya ke sayarwa ga rassan sa da ke sassan kasar nan.

A jawabinsa ga manema labarai, kakakin kungiyar Okanlawon Olanrewaju ya ce kamfanin NNPCL na son sayarwa da yan kasuwar man akan farashin naira dubu da naira 10 wanda kuma zai yi musu matukar wahalar gudanar da hada-hadar man a wanann farashi.

Karanta karin wasu labaran:Rikici ya kunno tsakanin NNPCL da Kungiyar kungiyar dillalan man fetur IPMAN

Tun farko IPMAN ta yi gargadin samun tsanantar rashin man a sassan Najeriya saboda abin da ta kira tsauraran matakan da NNPCL ke dauka.

Ƙungiyar ta IPMAN ta ce yanzu haka bashin bankuna ya yiwa mambobinta katutu saboda yadda NNPCL ke neman makuden kudade a hannunsu.

Kawo yanzu dai kamfanin na NNPCL ya baiwa dillalai da tsirarun yan kasuwa damar sayen man kai tsaye daga matatar Dangote.

A cewar IPMAN idan har yanayin da ake ciki a yanzu ya ci gaba, ko shakka babu Najeriya za ta afka matsanancin karancin man fetur.

Sau 4 kenan cikin watanni 16 gwamnatin Tinubu tana kara farashin man wanda kudinsa ya ninka idan aka kwatanta da yadda ake sayar da shi kafin hawan shugaba Bola Ahmed Tunibu karagar mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here