Yan ta’adda sun harbi shugaban tawagar tsaron al’umma ta Zamfara

0
79

Yan ta’adda sun harbi shugaban tawagar tsaron al’umma ta jihar Zamfara, Janar Lawal B. Muhammad mai ritaya.Janar Lawal B. Muhammad, ya samu damar tsallake rijiya da baya a hannun ’yan bindigar bayan sun harbe shi wanda bai kai ga kashe shi ba.

’Yan ta’addan sun harbi Janar Lawal, lokacin harin da suka kai kauyen Kucheri da ke karamar Hukumar Tsafe.

Wani jami’in rundunar tsaron ya tabbatar da  cewa, gaskiya ne ’yan bindiga sun harbi Darakta-Janar na Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Zamfara, a kwankwason sa, amma yana samun kulawa a asibitin awararru na Yariman Bakura da ke Gusau, bayan faruwar lamarin.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Zamfara ta biya tsaffin ma’aikata naira biliyan 9

A yammacin ranar Asabar ne yan ta’addan suka tare babbar hanyar Funtua zuwa Tsafe inda suka rika kai wa mutane hari, ciki har da Janar Lawal mai ritaya.

Maharan sun yi masa mummunan rauni sakamakon harbin da suka yi masa a kwankwason.

’Yan ta’addan sun kuma sace wasu matafiya da dama a yayin harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here