Za’a fara biyawa gawarwakin da ke ajiyewa haraji

0
91

Gwamnatin Enugu, tayi bayani akan shirin ta na fara karbar haraji akan masu ajiye gawarwaki a dakin ajiye gawa dake fadin Jihar.

A sanarwar da gwamnatin ta fitar tace ba dalilin tattara haraji ne yasa aka kafa dokar biyan kudin ba.

Shugaban hukumar tattara haraji ta Enugu, Emmanuel Nnamani, ne ya sanar da hakan a yau, yayin aikewa da umarnin fara karbar harajin zuwa ga masu Sana’ar adana gawarwaki.

Karanta karin wasu labaran:EFCC ta kama ‘yan damfarar intanet da dama a Enugu

Emmanuel Nnamani, yace tun a baya akwai Wannan doka ba yanzu aka kirkiro ta ba.

A kowacce rana za’a rika biyawa kowacce gawa daya naira 40, sabanin yadda wasu ke cewa dubu 40 za’a biya.

Gwamnatin Enugu, tace masu Sana’ar adana gawarwaki ne zasu rika biyan harajin ba iyalan mamatan da ake ajiyewar ba.

Idan za’a ajiye gawa tsawon kwanaki 100, za’a biya mata naira 4,000.

Emmanuel Nnamani, yace manufar samar da Wannan doka ita ce a tilastawa mutane rage al’adar ajiye gawa ba tare da binne ta ba, wanda hakan ya zama ruwan dare a tsakanin al’ummar Enugu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here