Ƙungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN zata yi wata ganawa da shugabannin matatar man fetur ta Dangote, a ranakun talata da Laraba, don Samar da tsayayyen farashin da matatar zata rika siyarwa yan kasuwa litar man.
IPMAN ta bayyana yarjejeniyar ta da matatar Dangote a matsayin wata babbar hanyar da zata taimakawa kasuwancin fetur da zirga zirgar sa a Nigeria.
A makon daya gabata ne gwamnatin tarayya ta bawa yan kasuwa damar siyo man daga Matatar Dangote, ba tare da kamfanin NNPCL ya shiga tsakanin su ba.
Bayar da umarnin baya rasa nasaba da rikicin da ya fara kunnowa tsakanin NNPCL da IPMAN akan zargin NNPCL da tsawwala farashin man bayan ya siya daya hannun Dangote.
Karanta karin wasu labaran:NNPCL ya bawa Matatar Dangote gangar mai miliyan 48
Chinedu Ukadike, yace suna maraba da tattaunawa da za’a yi tsakanin su da wakilan Matatar Dangote, don kulla alakar kasuwanci mai kyau a tsakanin su.
Matsalar man fetur dai ta zama wata babbar masifa ga yan Nigeria sakamakon yadda man ke zama wata hanyar karuwar tsadar rayuwa da sauran kuncin rayuwa.
Da farko al’ummar Nigeria sun yi zaton samun saukin farashin man bayan Dangote ya fara tace man a Nigeria sai dai abun ya bawa kowa mamaki bisa hujjar cewa fara aikin da matatar tayi bai kawo komai ba se karin tsadar man.