Gobara ta kone gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara

0
39

Gobara ta kone gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Bilyaminu Moriki da ke Gusau.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran, majalisar Bello Madaro ya fitar a Gusau ranar Lahadi.

Madaro ya bayyana iftila’in a matsayin jarrabawa.

A cewar sa gobarar ta lalata kadarori na miliyoyin Naira duk da cewa ba a yi asarar rai ba.

Aliyu ya bukaci kakakin majalisar da iyalansa da su dauki lamarin a matsayin kaddara.

Ya yi addu’ar Allah ya kiyaye faruwar lamarin a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here