Jam’iyyar NNPP zata ladabtar da gwamnan jihar Kano 

0
92

Tsagin shugabancin jam’iyyar NNPP karkashin Dr. Gilbert Agbo, masu adawa da tsarin kwankwasiyya sun Kona jajayen huluna da Kuma bayyana rashin amincewar su ga Kwankwaso a babban ofishin jam’iyyar dake Minna a jihar Niger.

Yan siyasar sun ayyana tsagin kwankwasiyya a matsayin babbar barazana ga cigaban NNPP.

Lokacin da yake jawabi a taron NNPP shiyyar arewa ta tsakiya, Agbo, ya jaddada dakatarwar da kwamitin jam’iyyar NNPP na kasa ya yiwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, lokacin taron jam’iyyar na Legas, wanda yace tun tuni an ayyana Kwankwaso a matsayin wanda bashi da katin jam’iyyar NNPP.

Karanta karin wasu labaran:NNPP ta sanar da mutanen da zasu yi mata takara a zabukan kananun hukumonin Kano

Dr. Gilbert, ya halarci taron magoya bayan da suka kona jar hula da sauran abubuwan dake nuna alamun goyon bayan Kwankwaso.

Sannan yace gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na NNPP saboda kin yin biyayya ga dokokin tsarin jam’iyyar.

Sai dai shugaban NNPP tsagin kwankwasiyya a jihar Niger Danladi Umar Abdulhamid, yace Agbo, ya yi kalaman sa don biyan bukatun kansa da kansa.

Yace har yanzu Kwankwaso shine jigon jam’iyyar NNPP a Nigeria

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here