Libya ta hana a kaiwa yan wasan Nigeria ziyara bayan sun shiga wani hali

0
105

Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu hukumomin Libya sun ki bawa tawagar ofishin jakadancin Nigeria damar ziyartar  ‘yan wasan Super Eagles da suka makale a filin jirgin saman kasar Libya.

MInistan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya ce yana bibiyar halin da tawagar Super Eagles ke ciki bayan hukumomin Libya sun sauya akalar jirgin tawagar ta Super Eagles zuwa wani karamin filin jirgi maimakon na Benghazi da aka tsara tun da farko jirgin zai sauka.

Ministan tace tun daga daren da ya wuce, ofishin jakadancin Nigeria a Libya ya yi ta magana da tawagar da kuma hukumomin Libya karkashin jagorancin Stephen Anthony Awuru.

Karanta karin wasu labaran:Yan wasan Nigeria sun yi barazanar kin buga wasa da Libya  

Jakadan yace duk kokarin da suka yi hukumomin Libya sun ki bayar da izinin zuwa birnin Bayda inda filin jirgin yake, don tattaunawa da yan kwallon.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta NFF ta ce yan wasan nata sun shafe kusan awa 15 suna jira a filin jirgin.

Kawo yanzu dai ba’a san dalilin kasar Libya na daukar Wannan mataki akan tawagar Super Eagles ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here