Rundunar yan sandan jihar Kwara ta sanar da korar jami’an ta 3 bisa zargin su da taka rawa a kisan wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar a babban birnin jihar Ilorin mai suna Qoyum Abdulyekeen Ishola.
Lamarin kisan daya faru ranar 4 ga watan Satumba ya samu kalubalanta da yin ala wadai, wanda hakan yasa aka mayar da binciken kisan zuwa babban birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin shugaban yan sandan kasa Kayode Egbetokun.
Karanta karin wasu labaran:Rikici ya kunno tsakanin gwamnan Rivers da shugaban yan sandan kasa
Jami’an da aka kora sun hadar da Abiodun Kayode, Samuel da Oni Philip.
Jami’ar hulda da jama’a na rundunar DSP Toun Ejire-Adeyemi, tace an samu jami’an da laifukan da suka shafi cin hanci da Kuma yin amfani da karfi a inda bai kamata ba.
Tace nan gaba kadan za’a gurfanar da jami’an da aka kora.
Rahotan jaridar Daily Trust, ya bayyana cewa an kashe dalibin lokacin zanga zangar karin farashin man fetur, da da