Bankin duniya yace dole yan Nigeria su jure wahalar garambawul a fannin tattalin arziki

0
183

Mataimakin shugaban bankin duniya Indermit Gill, yace akwai bukatar gwamnatin Nigeria ta cigaba da aiwatar da manufofin yin garambawul ga tattalin arzikin ta du da cewa yan kasar suna dandana kudar su, saboda hakan.

Sannan ya yabawa Bankin kasa CBN, da ya mayar da fannin sauyin kudin kasashen ketare mai dogaro da kansa ba tare da tallafin gwamnati ba.

Karanta karin wasu labaran:Tinubu ya memi hadin kan ‘yan kasuwa kan tattalin arzikin Najeriya

Mataimakin shugaban bankin duniyar, ya bayyana hakan a jiya lokacin da yake jawabi a wajen taron koli akan harkokin tattalin arzikin Nigeria wanda aka yi a Abuja.

Ya tabbatar da cewa manufofin gwamnatiin Tinubu na tattalin arziki suna cutar da al’umma musamman talakawa amma yace Wannan ita ce kadai hanyar da za’a bi  tattalin arzikin gwamnatin ya inganta.

A cewar sa nan gaba za’a ga amfanin wahalar da yan Nigeria suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here