Kashim Shettima zai tafi kasar Sweden

0
28

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, zai tafi kasar Sweden a yammacin yau laraba, don wakiltar Nigeria a wani taron da kasashen biyu suka shirya yi a tsakanin su.

Ana sa ran zai shafe kwanaki biyu a kasar, inda zai dawo Nigeria ranar asabar.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Stanley Nkwocha, cikin wata sanarwa daya fitar yace Shettima, zai halarci taron ne saboda shugaban kasa Tinubu baya nan.

Karanta karin wasu labaran:Ba za mu dora wa gwamnatin Buhari alhakin gazawarmu ba – Shettima

 A yayin ziyarar an ce zai gana da manyan jami’an gwamnatin Sweden, har ma da Fira ministan kasar.

Stanley, yace Shettima zai yi amfani da ziyarar wajen samarwa Nigeria alakar fadada ilimin fasaha da kirkire kirkire, aikin gona, sufuri, da hakar ma’adanai.

Sanarwar tace zai Kuma yi taro da yan kasuwa masu zuba jari daga Sweden, bayan tattaunawa da jami’an gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here