Yan bindiga sun kai sabon hari jihar Filato

0
75
Map-of-Plateau-State

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe mutune biyar a karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

An kashe mutanen a wani sabon hari da yan bindigar suka kai.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Bokkos, Farmasum Fuddang ne ya tabbaatr da faruwar hakan a ranar Talata.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa harin ya janyo mutuwar mutane biyar bayan kwantan baunar da yan bindigar suka yi.

Karanta karin wasu labaran:Yan bindiga sun kashe hakimi bayan garkuwa da shi a jihar Kebbi

Fuddang yace harin ya yi sanadiyyar rayukan matasa hudu wadanda suka fito domin tsare gidajensu.

 Bayan haka maharan sun kuma kashe wani tsoho bayan shiga  cikin gidansa.

Harin dai yazo kasa da mako daya da kai wasu hare hare, makamancin sa inda aka kashe wasu mutane goma a karamar hukumar ta hanyar yi musu kisan gilla.

Al’ummar yankin sun yaba wa jami’an tsaro bisa kokarinsu na fatattakar yan bindigar, inda suka yi kiran a  kara kokari tare da hadin gwiwa wajen dakile irin wadannan ayyukan rashin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here