Yan ta’adda zasu kaiwa al’ummar Zamfara harin ramuwa

0
89

Yan bindigar da suka addabi karamar Anka ta jihar Zamfara sun sha alwashin kaiwa al’ummar yankin hari, biyo bayan kama wani mutum mai kai musu makamai da bayanan sirri.Haka ne yasa mazauna karamar hukumar ta Anka da kewaye neman daukin gwamnati da jami’an tsaro kan barazanar kai masu harin.

Yan bindigar sun gargadi mazauna yankin tare da barazanar cewa, zasu kai musu hari a gidajen su da gonakin su don nuna fushin kama mai safarar makaman nasu.

Karanta karin wasu labaran:Gobara ta kone gidan kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara

Jami’an tsaron gwamnati ne suka kama wani mutum da aka tabbatar shine yake kaiwa yan ta’addan na Anka makamai a kwanakin baya.

Masanin sha’anin tsaron arewacin kasar nan, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa yan ta’addan sun yi gargadin ga mazauna karamar hukumar Anka a ranar 14 Oktoba, 2024. 

Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewacin Nigeria masu fama da matsanancin rashin tsaro, musamman yan fashin daji masu garkuwa da mutane, da kuma kisa babu dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here