APC ta musanta tsayar da mutane biyu takarar shugabancin karamar hukumar Danbatta

0
93

Jam’iyyar APC ta ce babu kamshin gaskiya a labarin da wasu ke yadawa dake nuni da cewa an fitar da yan takarar shugabancin karamar hukuma biyu a karamar hukumar Danbatta.

Da farko an samu wata takarda dake yawo inda aka bayyana Sunan Ibrahim Dan Bello, da cewa shine dan takarar shugabancin karamar hukumar Danbatta, sai wata takardar dake dauke da sunan Musa Sani Dambatta.

Karanta karin wasu labaran:APC ta nemi Ndume ya dena fitowa fili yana kalubalantar Tinubu 

Sai dai daraktan yakin neman zaben Musa Sani Dambatta, Usman Uba Sulaiman, ya ce ba haka batun yake ba, inda ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC Musa Sani Dambatta, ta tsayar Kuma shine cikakken dan takarar shugabancin karamar hukumar Danbatta.

Bayanin bangaren yakin neman zaben Musa Sani Dambatta, ya nemi al’umma suyi watsi da waccan sanarwa mai cewa Mansur Ibrahim Dan Bello, ne dan takara.

Idan za’a iya tunawa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC ta tsayar da ranar 26 ga watan da muke ciki don gudanar da zaben shugabannin kananun hukumomin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here