Memefi mining ne da ake yin sa a cikin Telegram Application, da kawo yanzu an shafe akalla watanni 7 ana yin sa.
Zuwa yanzu mutane miliyan 50 ne suka shiga mining din Memefi, yayin da mutane miliyan 28 da dubu dari 882 da 067 ke shiga cikin mining din a kowacce rana babu fashi.
An gina mining din Memefi akan Network din Linear layer-2 karkashin Blockhain na Ethereum.
Tun tuni Memefi suka yi launching bayanan su akan Network din Linear.
Karanta karin wasu labaran:Farashin kudaden Crypto zuwa Naira a yau Talata
Ana tara points din Memefi mai yawa ta hanyar gayyatar abokai zuwa cikin mining din, da yin Daily transaction na 0.2 Ton Coin, a kowacce rana inda za’a baka points miliyan 25 da 500 kowacce rana bayan kayi transaction din.
An tsara mining Memefi ta hanyar kashe wasu yan aljanu mataki zuwa mataki, a yanzu yawan daka mallaka yana taimakawa ka kai mataki mai nisa.
Sai kuma wani abu da ake cewa daily combo, ana samun points miliyan kullu a yanzu.
Zuwa Wannan lokaci an tsayar da ranar 30 ga watan Oktoba a matsayin lokacin yin listing Memefi coin, wato za’a fara yin kasuwanci a bisa ka’ida.
A baya dai mamallakan Memefi sun sanar da ranar 9 ga watan Oktoba da cewa zasu yi listing, sai dai sun bayyana dagewa inda suka ce wasu dalilai ne suka sanya dagawar.
Memefi sun ce zasu bayar da kaso 90 cikin dari na coins din su ga al’umma, wanda ake ganin hakan zai faranta ran wadanda suka yi mining din
YADDA ZAKA ZAMA ELIGIBLE
1 akwai wadanda suka siya Ton coin don yin transaction, wanda Memefi suka ce wadanda suka yi haka suna daga cikin mutanen da zasu samu airdrop din su kai tsaye, sai wadanda suka yi premium, shima da kudi a yin sa.
2 Sai wadanda za’a bawa coins din bayan yin mining ba tare da siyan komai ba.
3 Sune wadanda zasu samu Memefi ta hanyar wayar da kan mutane su shiga cikin mining din.
Bayan Wannan Memefi sun ki bayyana wasu ka’idojin da mutun zai cike wajen samun nasarar airdrop din nasu.
Daga cikin wadanda suka ce zasu iya fuskantar matsala akwai wadanda suka yi wasu abubuwan da Memefi basu amincewa ba da suka bayyana shi da (Cheat).
PRE-MARKET
A tsawon makonni 3 da suka gabata Exchange ta Bitget ta fara siyar da Memefi coins akan $ 0.03.
Kawo yanzu babu wata Exchange data bayyana wani abu akan Memefi bayan Bitget da ta fara yin Pre-market.
Amman Memefi sun kawo sabbin tasks na Binance da OKX, Exchanges, da ake kyautata zaton akwai yiwuwar Saka coins din a wadannan Exchanges.
In har da gaske za’a yi listing Memefi a ranar 30 ga watan Oktoba to ana sa ran su fitar da Lokacin kammala mining din daga yanzu zuwa ranar 25 ga wata.