Gwamnan Jigawa ya dakatar da kwamishinan da Hisbah ta zarga da lalata matar aure

0
23

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi, ya amince da dakatar da Auwalu Dalladi Sankara, daga mukamin kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman, biyo bayan zargin sa da yin lalata da matar aure da rundunar Hisbah ta jihar Kano tayi.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim, ya sakawa hannu.

Ya kuma jaddada kudirin yin aiki da rikon amana da kuma bin ka’idojin gudanar da mulki na Gwamna Malam Umar A. Namadi.

Karanta karin wasu labaran:Kwamishinan Jigawa ya karyata zargin lalata da matar aure.

 Yace an dakatar da kwamishinan don samar da adalci wajen binciken gaskiyar abin da ake zargin Auwalu Dalladi Sankara, da aikatawa

Jami’in hulda da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Ismail Ibrahim Dutse, ne ya fitar da sanarwar a yau.

Idan za’a iya tunawa a daren ranar alhamis data gabata ne aka samu labarin cewa rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani kwamishinan jihar Jigawa da zargin lalata da matar aure a Kano, bayan mijin matar ya kaiwa Hisbah korafi.

Auwal D Sankara, a safiyar yau asabar shine ya fara fitar da sanarwar musanta zargin, inda ya dauki alkawarin daukar matakan shari’a akan wadanda yace suna kokarin bata masa suna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here