Babban turken wutar lantarkin kasar nan ya durkushe karo na uku kenan cikin mako daya, wanda hakan ya jefa rayuwar al’umma cikin daukewar wutar baki daya a Nigeria.
Durƙushewar ta baya bayan nan ta faru da sanyin safiyar yau asabar, da misalin karfe 8:11.
Karanta karin wasu labaran:Yan Nigeria suna samun lantarki tsawon awanni 20 kowacce rana
A makon da muke ciki dai an samu durƙushewar babban turken wutar lantarkin da ta faru a tsakanin ranakun Litinin da Talata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa da misalin karfe 8 daidai na safiyar yau, akwai wutar lantarki mai karfin Megawatt 3,042, amma da karfe 7 karfin wutar yana megawatt 3,968, abin mamakin shine da misalin karfe 9 karfin wutar ya koma megawatt 47 kai tsaye.
Zuwa lokacin rubuta Wannan labari ba’a samu cikakken bayani akan sanadiyyar durÆ™ushewar ta yanzu ba, saboda an gaza samun karin haske daag kamfanin tattara lantarki na kasa TCN.