Adadin wadanda suka mutu a fashewar tankar man Jigawa sun haura 180

0
75

Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar tankar man fetur a ranar Talatar da ta gabata a garin Majia, dake jihar Jigawa, ya kai 180 zuwa ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba, kamar yadda mazauna garin suka shaidawa manema labarai.

Idan za’a iya tunawa lamarin ya faru a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba inda wata motar dakon mai data taso daga Kano zuwa Nguru a jihar Yobe ta fashe a garin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, sakamakon faduwar da ta yi, Kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100 nan take tare da jikkata wasu da dama.

Karanta karin wasu labaran:Kowanne gwamnan arewa ya bawa Jigawa tallafin naira miliyan 50 

Fashewar ta zama wani mummunan tashin hankali na farko a garin Majia, wanda al’ummar da abin ya shafa akasarin su manoma ne a jihar Jigawa da suka shahara wajen habaka tattalin arzikin noma a jihar.

Jabir Abdullahi Majia, wani mazaunin garin ya shaida wa Daily Trust cewa, mutanen da suka rasa ‘yan uwansu na ci gaba da jimami yayin da adadin wadanda suka mutu yake karuwa.

Ya kara da cewa, al’ummar yankin ba za su iya mantawa da wannan iftila’in ba, domin kusan kowane iyali lamarin ya shafa.

Tuni dai gwamnatin jihar Jigawa ta fara karbar tallafi daga daidaikun mutane da gwamnatoci don taimakawa wadanda iftila’in ya shafe, inda gwamnonin arewa suka bayar da tallafin naira miliyan 50 kowannen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here