Hisbah ta na neman Kwamishinan da ake zargi da lalata ido rufe

0
71

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bakin Kwamandan ta Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta bayyana kwamishinan jihar Jigawa Auwal D Sankara da ake zargi da lalata da matar aure Ruwa a Jallo.

Bayan an bada belinsa, an yi kokarin sulhu tsakanin bangarorin Kwamishinan da mijin matar, da yakai korafi amma Kwamishinan ya turo wani da sunan wakilinsa maimakon halartar zaman sulhun da kansa.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnan Jigawa ya dakatar da kwamishinan da Hisbah ta zarga da lalata matar aure

 Mijin matar ya nemi adalci, yana inda yake zargin Kwamishinan da kokarin neman umarnin kotu don gujewa kama shi. 

Ya kuma roki gwamnatin Kano, Sarkin Kano, da malamai su taimaka masa wajen yakar wannan zalunci da rashin amana da yake zargin an yi masa.

A ranar talata ne dai hukumar Hisbah ta kama Auwal D Sankara, kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa da zargin lalata da wata matar aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here