Kasar Masar ta kawo karshen zazzabin cizon sauro

0
32

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce kasar Masar ta yi nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro wanda aka fi sani da maleriya.

 Kokarin da Egypt tayi na kawar da cutar ya janyo mata yabo daga sannan duniya.

Shugaban majalisar dinkin duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa Cutar maleriya ta dade a kasar, amma yanzu an samu nasarar yakar ta baki daya.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Kebbi zata hukunta daliban kwalejin kiwon lafiya ta Jega

Kusan shekaru 100 da suka gabata kasar ta kaddamar da yaki da cutar zazzabin cizon sauro, wadda take kashe akalla mutum 600,000 duk shekara a duniya, mafi yawancin su a nahiyar Afrika.

A sanarwar, WHO, ta yaba wa Masar bisa kokarin da suka yi wajen yaki da cutar.

Sai dai a kasashe irin su Nigeria har yanzu cutar ta zazzabin cizon sauro tana cin karen ta babu babbaka, inda ko a yanzu haka cutar tana kan kashe mutane mafi yawancin su mata da kananun yara, duk da cewa mahukuntan kasar na cewa suna kan kokarin yakar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here