Rundunar sojin kasa ta karyata labarin mutuwar shugaban ta

0
45

Rundunar sojin kasar ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai wanda ke cewa, babban hafsan sojin kasa, COAS, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.

Rahotanni da dama da aka ruwaito daga wani dan jarida wanda ya wallafa a shafin sada zumunta, yana ikirarin cewa, babban hafsan sojin ya rasu.

Dan jaridar ya yi ikirarin cewa, Lagbaja ya mutu ne sakamakon cutar daji sa’o’i 48 da suka gabata a ranar Lahadi.

Karanta karin wasu labaran:Rundunar sojin Najeriya na neman mutum 8 ruwa-a-jallo kan kisan dakarunta a Delta

Sanarwar ta kara da cewa, Lagbaja ya mutu ne a wani asibiti da ba a bayyana ba dake Kasashen ketare kusan sa’o’i 48 da suka gabata daga mataki na uku na cutar daji.

Da take mayar da martani ga rahoton a shafinta na X, Rundunar Sojojin Nijeriya ta karyata rahoton inda ta ce, labarin karya ne wanda ba shi da tushe ballantana makama.

Sai dai wata majiya daga hedikwatar rundunar ta tabbatar wa da wakilin Punch cewa, babban hafsan sojojin na fama da matsanancin rashin lafiya.

Lambar wayar daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, tana kashe, kuma har zuwa loakcin rubuta wannan rahoto bai mayar da martani ga sakon da aka aike masa ba domin samun cikakken bayani kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here