Sanata Kwankwaso ya bayyana abinda ke faranta masa rai a siyasa

0
46

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, a zaben shekarar 2023, tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gudunmuwar  da yake bayar wa ga bangaren ilimi, shi ne abin da ya fi komai faranta masa rai a harkar siyasa.

Ya ce hidimta wa ilimi ya fi hanyoyi da gadojin sama da sauran ayyuka da ya yi a lokacin da ya mulki Jihar Kano.

Kwankwaso ya bayyana haka ne bayan bude sabon dakin taro a Jami’ar Skyline da ke Kano a matsayin wani bangare na murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya cika shekara 68 a yau 21 ga watan Oktoba.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnan Kano ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 68 a duniya

Kwankwaso ya kuma bayyana irin jin dadinsa na ganin yadda ayyukan da yayi a bangaren ilimi ke cigaba da yin tasiri ga al’umma.

Ya ce, yana yin matukar farin ciki idan ya ga mutanen da suka amfana da abubuwan da yayi sun zama manyan malaman da suke taimaka wa al’umma.

Ya tabbatar wa da mutanen Jihar Kano da Najeriya baki daya cewa zai ci gaba da tallafa wa ilimi domin inganta rayuwar mutane.

Rabi’u Musa Kwankwaso, shine gwamnan jihar Kano da ya taba samar da makarantar jami’a mallakin jihar har guda biyu a lokacin mulkin sa karo biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here