Sojoji sun ja kunnen masu son ayi juyin Mulki a Nigeria

0
97

Shalkwatar tsaron kasa ta gargadi mutane da kungiyoyi masu kira ga sojoji su yi juyin mulki a Nigeria, tare da jaddada cewa yin hakan cin amanar kasa ne a kundin tsarin mulki, kuma sojojin ba zasu yi wannan abu ba.

Hukumomin sojin sun kuma kara jaddada biyayyar su ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da kudurin kare tsarin dumukuradiyya.

Karanta karin wasu labaran:Juyin mulkin da muka yi har Najeriya muka ceta daga fadawa bala’in da ya tunkaro — Sojin Nijar

Bayanin hakan ya fito cikin wata sanarwa da shugaban sashin yada labarai na shalkwatar tsaron, Birigediya Janar Tukur Gusau ya fitar, inda ya ce sojoji za su ci gaba da mayar da hankali a kan babban aikin da ya wajaba a kansu, na kare yan kasa tare da tabbatar da zaman lafiya.

Ya kara da cewa ya kamata masu neman sojoji su yi juyin mulkin su sani cewa hakan da suke yi cin amanar kasa ne a bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Janar Gusau, ya kuma ce zaman lafiyar da aka samu a Nigeria a yanzu, ya samu ne sakamakon goyon bayan da shugaban Kasa ke ba wa sojoji da kuma jajircewar shugabannin sojojin.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa sojoji tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro za su dauki dukkanin matakan da suka dace wajen hana duk wani yunkuri na sauyin da ya sabawa kundin tsarin mulki.

Shalkwatar tsaron Nigeria ta fitar da wannan sanarwa bayan da aka samu wani hoton bidiyo a kwakin nan da wasu ke kira ga sojoji su yi juyin mulki.

Masu neman hakan suna ganin cewa mulkin sojoji zai iya kawo saukin halin kuncin rayuwa da ake ciki a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here