An samu raguwar amfani da man fetur a Nigeria

0
84
man fetur
man fetur

Adadin man fetur da ‘yan Nijeriya ke amfani da shi a kowace rana ya ragu tun bayan da Shugaba Bola Tinubu, ya soke tallafin man fetur.

Alkaluma sun nuna cewar ana shan lita miliyan 60 a watan Mayun 2024.

Amma a watan Agustan 2024, alkaluman sun sauya zuwa lita miliyan 4.5 a kowace rana.

Karanta karin wasu labaran:Har yanzu babu lokacin siyarwa yan kasuwa fetur daga matatar Dangote

Haka ne ya nuna cewar an samu raguwar man da ake sha wanda ya ragu da kashi 92 cikin 100.

Bayanan hukumar sun nuna cewa a cikin jihohi 36 guda 16 ne suka karbi mai daga kamfanin NNPCL wannan wata.

Kazalika, ya nuna cewar duk jihohin da ba su karbi mai daga kamfanin ba sun fuskanci karancinsa da dogayen layuka a gidajen mai.

Bayanai sun nuna cewar Jihar Neja ce ta fi samun mai da yawa, inda ta samu mota 21 kimanin lita 900,040 sai Jihar Legas da ta karbi mota 12 sama da lita 700,026, Jihar Kaduna an kai mata mota 12 kimanin lita 400,054.

Sauran jihohin da suka samu koma baya mafi yawa sun hadar da Oyo inda aka kai mata mota 12 dauke da lita 400,054 sai Kano mai mota tara, Kwara mota shida, Edo mota hudu, sai Babban Birnin Tarayya, Abuja mota hudu.

Tinubu ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu 2023, bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here