Kotun tarayya ta rushe shugabannin hukumar zaben Kano KANSIEC

0
38

Babbar kotun tarayya dake Kano ta rushe shugabannin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, nan take.

Kotun ta yanke hukuncin a yau 22 ga watan Oktoba 2024, bayan karar da Jam’yyar APC ta shigar.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana jam’iyyu 19 kawo wa KANSIEC matsala a zaben kananun hukumomin Kano

Bayanin hakan na cikin jawabin da kotun ta fitar bayan yanke hukuncin da maga takardan kotun Mohammed Iliyasu ya sakawa hannu.

Mai shari’a S.A. Amobeda, ne ya yanke hukuncin, inda yace ba’a bi wasu ka’idojin hukumar KANSIEC ba wajen bawa shugabannin mukamin.

Wannan abu yazo a daidai lokacin da ya rage kwanaki 4 a gudanar da zaben kananun hukumomin Kano a ranar 26 ga watan Oktoba.

Kotu tace wadanda aka bawa mukamin shugabannin hukumar basu cancanta saboda sun kasance magoya bayan jamiyyar NNPP mai mulkin Kano, dan haka kotun tace wadannan mutane basu da damar gudanar da zaben kananun hukumomin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here