Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya je Isra’ila don tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

0
64

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya sauka a kasar Isra’ila  don farfado da yarjejeniyar dakatar da bude wutar yaki a yankin Gaza da kuma tattaunawa kan sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

An shirya ziyarar bayan kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar, da Isra’ila ta yi, inda gwamnatin shugaban Amurka Biden ke ganin cewa akwai yiwuwar farfado da tattaunawar diflomasiyya a rikicin Gaza da Isra’ila.

Karanta karin wasu labaran:Isra’ila ta sake kaiwa Lebanon hari

Sai dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ba zai daina kai hare-hare ba har sai an kawo karshen Hamas.

Akwai yiwuwar Blinken zai mayar da hankali kan yadda za a mulki Gaza bayan rikicin, da barin kayan agaji su shiga arewacin Zirin Gaza.

Bayan Isra’ila, Blinken zai kuma tafi kasashen Larabawa a ci gaba da tattaunawar.

Ziyarar ta Blinken ita ce ta 11 a Gabas ta Tsakiya tun bayan fara yakin Gaza, da yayi sanadiyyar rasuwar mutane da yawa musamman falasdinawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here