Wasu fursunonin sun kammala karatun digiri a gidan gyaran hali 

0
66
Hands of the prisoner in jail

Wasu fursunoni guda goma sha daya daga gidan gyaran hali na Kaduna sun sami damar yin karatun digiri na farko da babbar Difuloma (PGD) daga Jami’ar NOUN.

Fursunoni bakwai sun kammala da kyakkyawan sakamako mai darajar Upper Second-Class, biyu sun samu Lower Second-Class, yayin da biyu suka sami takardun PGD.

Karanta karin wasu labaran:An zargi sojoji da kisan fararen hula a jihar Kaduna

 Wadannan fursunoni sun kammala karatunsu ne ta hanyar cibiyar NOUN da ke gidan gyaran halin cikin shekaru hudu zuwa biyar.

A lokacin wani karamin bikin yaye fursunonin da aka yi a gidan yari na Kaduna, wakilin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Dr. Baba, tare da Shugaban Kula da Gidajen gyaran hali na Jihar Kaduna, Nuru Mohammed Isah, ne suka mika takardun kammala karatun ga fursunonin.

Dr. Baba ya yabawa jarumtar fursunonin wajen kammala karatunsu duk da kalubalen da suka fuskanta a matsayin wadanda aka kulle.

Haka shima Mataimakin shugaban masu kula da Gidajen gyaran halin Abdullahi Dangani, ya gode wa NOUN bisa gudunmuwar da ta bayar wajen kyautata halayen fursunonin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here