Babban layin wutar lantarkin da ke kawo wuta Arewacin kasar nan ya sake lalacewa.
Shugabar sashin hulda da Jama’a ta Kamfanin Raba Wutar Lantarki Ndidi Mbah, ta ce sanar da hakan a safiyar Talata.
Karanta karin wasu labaran:Nigeria tana bawa Togo, Benin da Niger lantarki ta tsawon awanni 24
Sanarwar ta bayyana cewa wutar ta sake daukewa a ranar Lahadi, kasa da awa 24 bayan gyara layin a sakamakon daukewar da ya yi.
Ta bayyana cewa a halin yanzu akasarin yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na cikin duhu, da wani yankin na Arewa ta Tsakiya.
Karo na biyar kenan da babban layin wutar lantarkin ke lalacewa cikin mako biyu.
Mbah ta sanar da cewa manyan layukan wuta na 1 da na 2 da suke da karfin 330kv na lantarki da suka tashi daga Ugwaji zuwa Apir, sun katse, kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike domin gano hakikanin inda matsalar take domin gyarawa.