Yan bindiga sun kashe tare da yin garkuwa da mutane a Niger

0
65

Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yarinya ‘yar shekaru shida a Jihar Neja.

Rahotanni daga yankin Kotonkoro na karamar hukumar Mariga, sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun yi ta harbin motocin jama’a a daidai lokacin da fasinjoji ke kan hanyarsu ta shiga kasuwar garin.

Karanta karin wasu labaran:An samu raguwar amfani da man fetur a Nigeria

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunan sa ya ce, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane masu yawa ciki har da masu aiki a gonakin shinkafa.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Shehu Kotonkora ya ce, an kashe wani direban mota lokacin harin.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Wasi’u Abiodun, bai ce komai kan faruwar harin ba, kawo Wannan lokaci.

Amma shugaban karamar hukumar Mariga Hon. Abbas Kasuwar Garba, ya tabbatar da afkuwar harin.

Ya ce ‘yan bindigar sun fito daga dajin Zamfara, kasancewar yankin na da iyaka da jihohin Zamfara da Kebbi da kuma dajin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here