Za’a fara rubuta jarabawar WAEC da Computer a ranar juma’a

0
77

Hukumar tsara jarabawar kammala makarantun sakandire ta kasashen yammacin Afrika WAEC ta sanar da shirin sake rubuta jarabawar da na’ura mai kwakwalwa wato computer karo na biyu, da za’a fara daga ranar juma’a 25 ga watan Oktoba zuwa 20 ga watan Disamba na shekarar da muke ciki.

Karanta karin wasu labaran:Yan wasan Kano Pillars sun yi hatsari a hanyar zuwa Jos

Mai magana da yawun hukumar WAEC Moyosola Adesina, ne ya sanar da hakan a yau Talata.

Sanarwar da ya fitar tace an kara wa’adi yin rijistar jarabawar zuwa ranar 29 ga watan Oktoba.

Sai dai yace dalibai suna da damar zabar rubuta jarabawar a takarda da biro, ga wanda baya sha’awar yin amfani da computer.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here