Shugaban kamfanin siyar da man fetur na Rainoil, Gabriel Ogbechie, ya nemi yan Nigeria su shiryawa ganin wani sabon farashin litar man.
Yace nan gaba kadan yan Nigeria zasu fara siyan man fetur a cikakken farashin sa ba tare da tallafin ko kwandala ba, biyo bayan janye hannun gwamnati akan harkar karawa ko rage farashin, wanda hakan ya faru saboda aiwatar da dokar man fetur ta kasa bayan shugaban kasar ya cire tallafin man fetur.
Karanta karin wasu labaran:An samu raguwar amfani da man fetur a Nigeria
Gabriel ya sanar da hakan a jiya lokacin da ake zantawa dashi a kafar talbijin ta Channels.
A lokacin da Tinubu ya cire tallafin man fetur, man ya tashi daga farashin 198, zuwa 545, amman a yan kwanakin nan ana siyar da man akan farashin naira 1250.