Gwamnatin tarayya zata hukunta jihohin da basu yi zaben kananun hukumomi ba

0
24
Tinubu

Gwamnatin tarayya ta ce za ta dauki mataki a kan jihohin da suka ki gudanar da zaben ƙananan hukumomi da zai tabbatar da cin gashin kai na kananan hukumomin kamar yadda hukuncin kotun kolin ya umarta

Babban lauyin gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Lateef Fagbemi, ne ya bayyana hakan a jihar Ekiti a jiya Talata.

Karanta karin wasu labaran:Majalisar dokokin Kano tace babu abinda za’a hana zaben kananun hukumomi

Ya ce ba gudu ba ja da baya a kan shirin aiwatar da hukuncin kotun kolin na cin gashin kananan hukumomin.

Fagbemi ya ce gwamnatin za ta yi nazarin dokokin jihohi a kan zaben kananan hukumomi tare da duba dalilin da ya sa wasu jihohin suke yin jinkirin gudanar da zaben.

Bayanai sun nuna cewa a yanzu sama da kananan hukumomi 164 ne a jihohi takwas ba’a yi zaben ba.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa, wasu rahotanni na nuna cewa mai yiwuwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da hukuncin kotun kolin a kan cin gashin kai na kananan hukumomi a karshen watan Oktoba.

Hakan na nufin gwamnatin tarayya za ta iya rike kason kudin kananan hukumomin da ba a yi zabe ba, kamar yadda hukuncin kotun ya ayyana.

Ƙananan hukumomin da ba a yi zabe ba sune na jihohin Katsina da Zamfara da Nasarawa Ondo, da Osun da Ogun da Cross Rivers, da Kano.

Hukuncin kotun ya nuna ce, saba doka ne gwamnonin jihohi su ci gaba rike kason kudin kananan hukumomi a karkashin asusun hadin gwiwa na jiha da kananan hukumomi.

Wasu gwamnonin jihohin dai na ganin cewa hukuncin bai yi musu dadi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here