Sojojin Nigeria biyar sun mutu a hatsarin mota

0
52
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Wasu sojojin saman kasar nan biyar suna daga cikin matafiya 19 da suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku a Hawan Kibo da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Hatsarin ya faru a jiya Talata.

Karanta karin wasu labaran:Sojoji sun ja kunnen masu son ayi juyin Mulki a Nigeria

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama Olusola Akinboyewa ya fitar, ya ce, sojojin sun yi hatsari a kan hanyar su ta zuwa wani wasa a Abuja, lokacin da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.

Sai dai kuma wani bayani da hukumar kiyaye hadura ta kasa ya saba da wanda kakakin sojin ya fitar, inda hukumar ta ce motar bas ta sojojin kirar Hiace, mai daukar mutum 18 da ta taso daga Yola ta bi yo ta Jos a kan hanyarta ta zuwa Abuja ta ci karo ne da tirela wadda ke tsaye a kan hanya, lamarin da ya janyo mutuwar direban da dukkanin sauran mutanen da ke cikin motar su 18.

A wata hira da tashar talabijin ta Channels, kakakin hukumar ta kiyaye hadura (FRSC) a jihar ta Filato, Peter Longsan, ya ce dukkanin mutanen da ke cikin wannan mota da sojojin suke ciki sun mutu.

Longsan ya danganta munin hadarin da ya kai ga mutuwar mutanen gaba daya, da gudun da direabn sojojin ke yi inda ya ce a dalilin hakan ne ta yi karo da babbar motar tirelar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here